Kamfanin dilalncin labaran ikna ya nakalto daga shugaban bangaren kula da shirya tarukan tunawa da zagayowar ranar haihuwar Imam Hujja AJ a Iran cewa; Bayyana r Imam Mahdi AS shi ne babban abin zai kawo karshen zalunci da danniya tare da tabbatar da adalci a doron kasa. A cikin akidar addinin musulunci Imam Mahdi wani mutum mai matukar daraja da matsayi wajen ubangiji, wanda zai bayyana a karshen zamani domin kubatar da duniya daga zalunci da danniyar kasashe masu girman kai, tare da tabbatar da adalci a doron kasa, da kuma kyautata rayuwa ta zamnatakewar jama'a
444994