Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dilalncin labaran Iba cewa; An fara gudanar da tarukan watan sha'aban da aka saba gabatarwa a kasar Kuwait duk kowace shekara, da hakan ya hada da gabatar da tarukan maulidin Imam Hussain da kuma Abul fadl abbas, da ake gudanarwa a Husainiyar ja'afariyyah da ke birnin Kuwait. Bayanin ya ci gaba da cewa an samu halartar mutane a wannantaron maulidi mai albarka, kamar yadda masu rera wakokin yabon iyalan gidan manzon Allah da kuma masu gabatar da jawabai. Da dama daga cikin wadanda suka halarci taron sun nuna farin cikinsu maras misiltuwa.445132