Bangaren al'adu da fasaha; An gudanar da wani taro da ya kebanci kur'ani da koyarwarsa a cikin al'ummar musulumi da kuma yadda ya kamata a misiltu da wannan koyarwar, wanda ya kebanci mata.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; An gudanar da wani taro da ya kebanci kur'ani da koyarwarsa a cikin al'ummar musulumi da kuma yadda ya kamata a misiltu da wannan koyarwar, wanda ya kebanci mata. Bayanin ya ci gaba da cewa Kwamitin wanda ya hada kungiyoyi da cibiyoyin addinin musulmunci sama da 40 daga sassa daban-daban na kasashen duniya, zai yi dubi ne a zaman nasa na birnin Tripoli kan muhimman batutuwa da suke ci ma al'ummar musulmi tuwo a kwarya a cikin wannan zamani, da hakan ya hada da cin zarafin da ake yi wa musulmi da mabiya addinin musulunci a wasu kasashe na yammacin turai, tare da daukar matakan da suka dace da nufin kawo karshen hakan.445356