Kamfanin dilalncin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar kasar saudiyya ta Alwatan cewa; Za a gudanar da hardar karatu da gasar karatun kur'ani mai tsarki a yankin Qatif na kasar saudiyya, inda mahardata da makaranta kur'ani mata za su halarci taron gasar. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasa na daya daga cikin tarukan gasar kur'ani mai tsarki da ake shiryawa a kasar saudiyya a yankin katif na mabiya mazhabar shi'a a kowace shekara.
445795