Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren yada labarai da hulda da jama'a na cibiyar kula da al'du da yada ilimin Musulunci ta kasar Iran Mahdi Mostafavi cewa; Jiran bayyanar limamin zamani kuma hujjar ubangiji a bayan kasa, wata fitila ce da ke dauke da haske mai haskaka hanya ga muminai masana hakkokin iyalan gidan manzon Allah SAW a kansu a kowane zamani. Bayanin ya ci gaba da cewa manufar gudanar da tarukan ita ce kara wayar da kan musulmi dangane da muhimamncin da ke tattare da raya harkokin karatun kur'ani a ko'ina cikin kasashen musulmi.
446764