Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga cibiyar yada manufofin bayyanar limamin zamani AJ cewa; Akidar yin imani da bayyanar Imam Mahdi na nufin imani da kafuwar adalci da gaskiya tare da kawo karshen zalunci da danniya a kan raunana a duniya, tare da tabbatar da huknce-hukuncen ubangiji kamar yadda Allah yake bukatar bayinsa da su bi domin samun tsira da kuma rahmarsa a ranar karshe. Bayanin ya ci gaba da cewa jiran limamin zamani shi kansa na tattare da wasu hikimomi da dukkanin biladama suke amfanuwa da su a halin sani ko rashinsa.446639