Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga shafin internet na cibiyar kula da harkokin musulmi a kasar Danmark cewa; Musulmin kasar Danmarka sun yi kakakusar suka dangane da aniyar da mai zane-zanen batuncin nan na kasar yake da ita wajen sake yin wani zanen domin yin batunci ga ma'aiki SAW. Bayanin ya ci gaba da cewa mutumin na shirye-shiryen sake watsa wani zanen batunci ga addinin muslunci a cikin 'yan lokutannan, lamarin da ke ci gaba da fuskantar fushin musulmi.
446447