Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Nasij cewa; Dan majalisar kasar Holland din nan mai tsananin gaba da addinin Musulunci da kuma musulmi na neman a dauki matakin dakatar da karuwar musulmi a nahiyar turai. Wannan dai ba shi ne karon farko da wannan dan majalisa mai tsananin gaba da Musulunci yake yin hankoron ganin an takura musulmi a nahiyar turai ba, amma dukaknin kungiyoyin musulmi na yin iyakacin kokarinsu domin ganin an taka masa birki dangane da wananan mummunan mataki nasa.
447343