Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran ZAMAN cewa; An gudanar da taron maulidin Imam Hussain a garin kadikoy da ke kasar Turkiya, a babbar Husainiya da ke birnin, taron day a samu halartar malaman addinin masoya iyalan gidan manzon Allah da dama. Bayanin ya ci gaba da cewa an gudanar da taron a ranar lahadi da ta gabata, inda aka gabatar da laccoci da nufin karfa musulmi mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da ma duk mai son jin tarihin Imam Hussain da yadda rayuwarsa ta kasance da sauran iyalan gidan manzon Allah SAW da suka rayu tare da shi a zamanin imamancinsa.
447139