Bangaren fasaha; Masu kula da palastinawa 'yan gudun hijira a sansanoninsu da ke cikin kasashen larabawa sun fara gudanar da taronsu domin dubi dangane da halin da palastinawa ke ciki sansanoninsu a birnin Alkahira na kasar Masar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran sana na kasar Syria cewa; Masu kula da palastinawa 'yan gudun hijira a sansanoninsu da ke cikin kasashen larabawa sun fara gudanar da taronsu domin dubi dangane da halin da palastinawa ke ciki sansanoninsu a birnin Alkahira na kasar Masar. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro ana gudanar da shi ne a kowace a daya daga cikin kasashen larabawa, domin tattauna muhimman abubuwan da palastinawa suke bukatar taimako a kansa. Daga cikin wadanda suke halartar wanda aka fara gudanarwa a birnin alkahira na kasar Masar, akwai wakilan kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC.
447155