IQNA

Sojojin Syria Sun Kwace Wasu Yankuna Masu Matukar Muhimmanci Daga 'Yan Ta'adda

11:54 - October 27, 2013
Lambar Labari: 1816
Bangaren kasa da kasa, Rahotanni daga kasar Syria sun ce dakarun kasar sun samu nasarar kwace iko da wasu yankuna masu matukar muhimamnci daga hannun mayakan ‘yan bindiga, bayan kwashe tsawon kawanaki ana gumurzu tsakanin bangarorin biyu.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, dan rahoton tashar talabijin ta Al-alam daga kasar Syria wanda ya kasance tare da sojojin na Syria ya bayar da rahoton cewa, dakarun na kasar Syria sun yi wa daruruwan bindiga kofar raggo a yankunan Hatita Turkman da ke karakshin iko ‘yan bindiga wadanda kasashen yamamcin turai gami da Saudiyya da Qatar suke marawa baya, inda suka samu nasarar kashe adadi mai yawa daga cikinsu, wasunsu kuma suka tsere, inda ya zuwa yammacin jiya dukkanin yankunan Hatita suka dawo karshin ikon hukuma.



Wasu rahotannin kuma daga kasar ta Syria sun tabbatar da cewa a jiya an yi wata musayar wutar mai tsanani tsakanin mayakan kurdawa da kuma ‘yan alka’ida a a kan iyakokin Syria da Iraki, bayan da ‘yan alkaida suka nemi shiga cikin kasar ta Syria ta kauyen Ya’arabiyya da ke kan iyakar Syria da Iraki, wanda galibin mazauna cikin sa Kurdawa ne, rahoton ya ce mayakan kuradawan sun hallaka mayakan alkaida da dama, lamarin da ya tilasta su komawa cikin kasar ta Iraki.



Jami'an Pentagon sun bayyana cewa Sojojin da za su tura za su bayar da horo ne kan rundunoni na musaman masu yaki da 'yan ta'adda.



A farkon wannan wata na Octoba komododin Amurka sun kai farmaki a kasashen Libiya da Somaliya kan fakewar fada da 'yan ta'adda.



 



Manazarta na ganin cewa kasar ta Amurka na da wata manufa ta musaman a nahiyar ta Afirka wanda ya sha baban kan irin ikrarin da take yi na yaki da 'yan ta'adda ganin cewa wannan garni na 21 garni da aka bashi taken Nahiyar Afirka,manazarta na ganin cewa babar manufar Amurka a wannan nahiya shine kokkayyar tattalin Arziki tare da kasashen Birtaniya da Faransa tare da kokarin hana fadadar alakar kasuwanci tsakanin Nahiyar da kasar China.



 



A wannan shekara kasar ta Amurka tace za ta aika Sojoji 3500 zuwa nahiyar ta Afirka kan fakewar bada horo ga Sojojin na Afirka tare da kara masu sani kan sabin makaman zamani.



Ko da yake Gwamnatin ta Amurka ta rake abinda ta ke kashewa a bangaren Soja a wannan Nahiya manazarta na ganin wannan na daga cikin abinda ya sanya Sojojin Amurka shiga nahiyar kai tsaye.



1307068


Abubuwan Da Ya Shafa: bangaren
captcha