Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa makarancin kur'anin dan kasar Iran Mas'ud Pirozzmand da ya isa kasar Kenya ya gabatar da karatun kur'ani mai tsarki da aka sanya kai tsaye a gidan radiyon kasar Kenya daga garin Mambasa. Bayanin ya ci gaba da cewa gidan radiyon Rahma na birnin Mambasa shi ne ya gayyaci makarancin domin gabatar da kira'a a gidan radiyon, wanda ya tashi takanas zuwa kasar domin karba wannan goron gayyata.
463201