IQNA

Kwamitin Fatawar Musulunci A Turai Ya Sanar Cewa Ranar Lahadi Ce Ranar Idi

16:58 - September 12, 2009
Lambar Labari: 1825194
Bangaren kasa da kasa; Babban kwamitin malaman addinin Musulunci masu fitar da fatawa a nahiyar ya sanar da ranar Lahadi ta makon gbe a matsayin ranar idin karamar salla.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na Islam online cewa; kwamitin malaman addinin Musulunci masu fitar da fatawa a nahiyar ya sanar da ranar Lahadi ta makon gbe a matsayin ranar idin karamar salla. Bayanin ya ci gaba da cewa bisa la'akari da cewa ranar Asabar ce watan Ramadan zai kawo karshe wato rana ta 29, wannan ya sanya kwamitin sanar da ranar Lahadi a matsayin ranar idi da dukkanin musulmi a nahiyar turai za su gudanar da bukukuwan karamar salla. Haka nan kuma ana sa ran mafi yawan kasashen musulmi za su gudanar da bukukuwan karanmar salla ne a wannan rana.
463558

captcha