Kamfanin dillancin labaran Iqnq ya nakalto daga daga bangaren yada labaransa na kasar India cewa; An gudanar da tarukan lailatul qadr a garuruwan kasar India, daga ciki kuwa har da babban birnin kasar New Delhi. Bayanin ya ci gaba da cewa tarukan sun samu halartar musulmi da suka hada mabiya mazhabar shi'a da kuma 'yan sunna, inda suka kwana yin ibada da karatun kur'ani mai tsarki da kuma yin salloli. Wannan na daya daga cikin abin da muslmin India ke yi kowace shekra. 463666