Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran biladi cewa; An gudanar da wani babban taro na buda baki a birnin Katalonia na kasar Spain, wanda ya samu halartar mabiya addinan musulunci da na kiristanci da ma jami'an gwamnati. Bayanin ya ci gaba da cewa an gudanar da wannan taron ne domin nuna dukkanin mabiya addinai cewa addinin musulunci addini ne na 'yan adamtaka da kaunar sauaran addinai, kamar yadda dukkanin wadanda suka halarci buda baki suka nuna matukar sha'awarsu dagamsuwarsu da hakan.463633