A cikin wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Iqna da wasu jami'an huldar diplomasiyar Iran a kasar Afghanistan, Jakadan jamhuriyar musulunci ta Iran a kasar Afghanistan ya bayyana cewa akwai wani shiri na musamman da za a gudanar tsakanin kasashen Iran da Afghanistan na karatun kur'ani a cikin kasashen biyu. Fada Hossain Maliki ya ci gaba da cewa kasashen Iran da Afganistan kasashe ne biyu masu tsohuwar danganataka ta tarihi da al'adu da kuma addini guda, wanda babu wani abin da zai iya raba kasashen biyu. A kan haka za su ci gaba da gudanar shirye-shirye na addini na hadin gwiwa tsakaninsu.463200