IQNA

Al'ummar Musulmi Na Bukar Yin Aiki Da Kur'ani Cikin Rayuwar Zamantakewa

Bangaren rahoto; Al'ummar musulmi na bukatar yin aiki da kur'ani mai tsarki a cikin dukkanin harkokin rayuwarsu na zamantakewa, kuma babu wani wanda ke musun hakan.
A cikin wata zantawa da ta hada daya daga cikin malaman addinin muslunci a Iran Sayyid Fadil Nasiri ya bayyana cewa; Al'ummar musulmi na bukatar yin aiki da kur'ani mai tsarki a cikin dukkanin harkokin rayuwarsu na zamantakewa, kuma babu wani wanda ke musun hakan. Ya ci gaba da cewa alkura'ni shi ne tsarin rayuwa da ya dace da dan adam, a kan haka wannan yana tabbatar da cewa shi ne tsarin da ya fi dacewa da muslmi su rungume shi, domin kuwa su ne suka fi kowa kusa da kur'ani, domin kuwa wannan ne zai kara kyautata zamantakewarsu.463493