Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga jaridar The News ta kasar Pakistan cewa; An gudanar da tarukan tunawa da zagayowar ranar shahadar Imam Ali (AS) a birnin Lahore na kasar Pakistan, inda taron ya samu halartar dubban musulmi mabiya mazhabar Ahlul bait. Bayanin ya ci gaba da cewa an gudanar da taron ne a lokacin da kasar take cikin wani hali na dadarniya, sakamakon hare-haren da 'yan ta'adda suke ci gaba da kai kan mabiya mazhabar Ahlul bait a kasar, amma duk da wannan baraza dubban mutane sun halarci tarukan. 463943