IQNA

Za A Bude Baje Kolin Rubuce-Rubucen Kur'ani A Birnin Dubai

8:44 - September 14, 2009
Lambar Labari: 1825805
Bangaren kasa da kasa; Za a bude wani babban taro da zai hada da hada da baje koli na rubuce-rubucen kur'ani mai tsarki mafi kyau na kasa da kasa a birnin Dubai na hadaddiyar daular larabawa.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar hadaddiyar daular larabawa cewa; Za a bude wani babban taro da zai hada da hada da baje koli na rubuce-rubucen kur'ani mai tsarki mafi kyau na kasa da kasa a birnin Dubai na hadaddiyar daular larabawa. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro zai samu halartar marubuta, musamman ma masu rubutun hannu da suke rubuta alkur'ani da kuma alluna da ke dauke da ayyin kur'ani mai tsarki, tare da kuma halartar manyan jami'an gwamnatin kasar. 463929








captcha