A wata zanatawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Iqna reshen kasar Afghanisan da minista mai kula da harkokin addinin Musulunci a kasar Afghanistan Damin Ali Ahmad ya bayyana cewa; ana samun ci gaba matuka a kasar wajen kara yaduwar ilmomin kur'ani. Ya ci gaba da cewa yanzu haka dai kasarsa a shirye take ta kara samun gogewa yadda ya kamata daga kasashen musulmi dangane da dukkanin ilmomi da suka danganci kur'ani mai tsarki. Ya ce ana samun ci gaba tsakanin al'ummar kasar matuka ta fuskacin kara sanin kur'ani mai tsarki da karatunsa da hardarsa da ma fahimtar ma'anoninsa. 463995