IQNA

Afghanistan Za Ta Iya Zama Wata Cibiyar Yada Koyarwar Kur'ani

8:44 - September 14, 2009
Lambar Labari: 1825808
Bangaren kasa da kasa; Shugaban cibiyar kula da harkokin addini da al'adu ta kasar Iran reshen Afganistan Nasir jahan shahi ya bayyana cewa; Afghanistan za ta iya zama wata babbar cibiyar yada koyarwar kur'ani a cikin kasashen musulmi.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga bangarensa na na birnin kabu cewa; Shugaban cibiyar kula da harkokin addini da al'adu ta kasar Iran reshen Afganistan Nasir jahan shahi ya bayyana cewa; Afghanistan za ta iya zama wata babbar cibiyar yada koyarwar kur'ani a cikin kasashen musulmi. Ya ci gaba da cewa yanzu haka dai kasar a shirye take ta kara samun gogewa yadda ya kamata daga kasashen musulmi dangane da dukkanin ilmomi da suka danganci kur'ani mai tsarki. Ya ce ana samun ci gaba tsakanin al'ummar kasar matuka ta fuskacin kara sanin kur'ani mai tsarki da karatunsa da hardarsa da ma fahimtar ma'anoninsa. 463975



captcha