IQNA

An Gudanar Da Taron Buda Baki A Cibiyar Musulunci Ta Holland

16:38 - September 15, 2009
Lambar Labari: 1826644
Bangaren kasa da kasa; An gudanar da wani gagarumin buda baki a babban ginin cibiyar musulunci ta kasar Holland da ke birnin Rotterdam.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran resalthaber cewa; An gudanar da wani gagarumin buda baki a babban ginin cibiyar musulunci ta kasar Holland da ke birnin Rotterdam. Bayanin ya ci gaba da cewa taron wanda cibiyar ta dauki nauyin shiryawa, ya samu halartar manyan baki da suka hada jami'an gwamnati da 'yan majalisar dokokin kasar, gami da manyan malaman musulumi. An kafa wannan cibiya kimanin shekaru arba'in da suka gabata, kuma tana gudanar da shirye-shiryenta na musulunci.464552


captcha