IQNA

Manufar Aiko Manzanni Ita Ce Kusantar Da Mutum Zuwa Ga Allah

16:37 - September 15, 2009
Lambar Labari: 1826647
Bangaren kasa da kasa; Babbar manufar aiko manzanni daga Allah ita ce shiryar da mutum tare da kusantar da shi zuwa ga Allah madaukakin sarki,
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga bangaren yada labaransa na birnin Tehran cewa; a wani zaman buda baki da aka gudanar jiya, wanda ya samu halartar manyan jami'an gwamnatin Iran a birnin Teharan, an gudanar da bayanai kan manufar azumi dav kuma amfaninsa ga mutum, a yayin gudanar da taron, daya daga cikin malaman da suka gudanar da bayanai ya bayyana cewa; Babbar manufar aiko manzanni daga Allah ita ce shiryar da mutum tare da kusantar da shi zuwa ga Allah madaukakin sarki, tare da bashi tarbiya da ta dace da shi a matsayins ana bawan Allah.464557


captcha