IQNA

Za A Gudanar Da Taron Girmama Wadanda Suka Halarci Gasar Kur'ani A Masar

13:50 - September 16, 2009
Lambar Labari: 1827038
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani babban taro domin yin ban girma ga makaranta da mahardatan kasar Masar da suka shiga cikin gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa da aka gudanar a birnin Alkahira.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran Nasij cewa; Za a gudanar da wani babban taro domin yin ban girma ga makaranta da mahardatan kasar Masar da suka shiga cikin gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa da aka gudanar a birnin Alkahira. Bayanin ya ci gaba da cewa za a gudanar da taron girmama wadannan mutane ne ne a babban dakin gudanar da taruka na babbar jami'ar nan ta Alazhar a birnin alkahira fadar mulkin kasar ta Masar, taron da zai samu halartar malamai gami da wasu manyan jami'an gwamnatin kasar.465166captcha