IQNA

Za A Gudanar Da Gasar Harda Da Karatun Kur'ani A Birtaniya

13:50 - September 16, 2009
Lambar Labari: 1827042
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki a babbar cibiyar musulmi mazauna birnin Nanten na kasar Birtaniya, wadda za ta kebanci mata musumi kawai.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na Albirr cewa; Za a gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki a babbar cibiyar musulmi mazauna birnin Nanten na kasar Birtaniya, wadda za ta kebanci mata musumi kawai. Bayanin ya ci gaba da cewa; yanzu haka an kammala dukkanin shirye-shiryen da suka kamata domin gudanar da wannan gasar karatun kur'ani mai tsarki. Gasar za ta samu halartar matasa musulmi mata da suka hardace kur'ani mai tsarki ko kuma suka hardace wani bangarensa, daga sassa daban-daban na kasar Birtaniya. 465116




captcha