Daga kudu maso gabacin Asiya ne cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ne ta watsa rahoto bayan ta nakalto daga jaridar Iktisadiya ta Saudiya da ke cewa; karkashin wannan shawara da aka bayar kan fassara kur'ani mai girma da zai karawa musulmin kasar sanin kur'ani inda a cikin garuruwa hamsin da shidda a jahar Jauhar za fassara kur'ani da kuma rarraba su a tsakanin musulmin yankin. Ministan jahar ta Jauhar a Malaishiya kan wannan lamari ya bayyana cewa; wannan shawara da ta shafi fassara kur'ani tana karkashin wani shiri na musamman kan Al'adu ta inganta ilimi da sani kan kur'ani mai tsarki.
465907