IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Kur'ani A Birnin Kashan

Bangarenfasaha; Gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin Kashan kasar Iran, wanda kuma wannan shi ne karo na biyar da ake gudanar da irin wannan gasa a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na arabonline cewa; An fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin Kashan na kasar Iran, wanda kuma wannan shi ne karo na biyar da ake gudanar da irin wannan gasa a kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa gasar tana samun halartar makaranta da kuma mahardata kur'ani mai tsarki daga kasashen musulmi daban-daban. shugaban kula da karun kur'ani ne ke jagorantar gudanar da tarukan gasar a binin Kashan. 467265