Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga bangaren yada labaransa na birnin Tehran cewa; a wani zaman buda baki da aka gudanar jiya, wanda ya samu halartar manyan jami'an gwamnatin Iran a birnin Teharan, an gudanar da bayanai kan manufar azumi dav kuma amfaninsa ga mutum, a yayin gudanar da taron, daya daga cikin malaman da suka gudanar da bayanai ya bayyana cewa; Babbar manufar aiko manzanni daga Allah ita ce shiryar da mutum tare da kusantar da shi zuwa ga Allah madaukakin sarki, tare da bashi tarbiya da ta dace da shi a matsayins ana bawan Allah.466890