Kamfanin dillancin labaran Iqnq ya nakalto daga bangaren watsa labaransa na kasar Pakistan cewa; Ofishin al'adu na jamhuriyar musulunci ta Iran a birnin Karachi an kasar Pakistan na gudanar da shirye-shiryen watan Ramadan kamar yadda ya saba a a kowace shekara. Shugaban ofishin cibiyar kula da al'adu ta jamhuriyar musulunci ta Iran a Pakistan shi ne ya bayyana hakan, inda ya ce suna gudanar da dukkanin shirye-shirye da suka danganci wannan wata mai alfarma.466500