IQNA

An Fara Gudanar Da Taron Makon Kur'ani A kasar Indonesia

11:27 - September 20, 2009
Lambar Labari: 1828052
Bangaren kasa da kasa; An bude taron makon kur'ani a birnin Jakarta na kasar Indonesia, tare da halartar wasu daga cikin jami'an huldar diplomasiyar kasar Iran da ke birnin.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga daga wakilinsa a birnin Jakarta na kasar Indonesia cewa; An bude taron makon kur'ani a birnin Jakarta na kasar Indonesia, tare da halartar wasu daga cikin jami'an huldar diplomasiyar kasar Iran da ke birnin da kuma wakilin jami'ar Mostafa. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan dai ba shi karon farko da ake gudanar da irin taro a birnin ba, amma a wannan karon taron ya dauki sabon salo saboda sabbin shirye-shiryen da aka bullo da su domin kara karfafa gwiwar mahardata da makaranta kur'ani mai tsarki na kasar Indonesia. 466949
captcha