Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin infomaroc cewa; Za a gina wata cibiyar al'adu ta Musulunci a kasar China domin amfanin masu yawan bude idanu a kasar, wadda za a gina a yankin Nichina na arewacin kasar nan ba da jimawa ba. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan cibiya za ta kunshi wasu bangarori na bayar da ilimi da bada horo kan tarihin muslunci da al'adunsa, kamar yadda za ta kunshi dakin kayan tarihi.466848