IQNA

An Bude Baje Kolin Kayan tarihin Musulunci A Kasar Girka

Bangaren al'adu da fasaha; A karon farko an bude wani baje kolin kayan tarin Musulunci da suke da dangantaka da birnin Qods mai alfarma da kuma masallacin aksa, da nufin raya ranar Qods ta duniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga wasu kafofin yada labarai cewa; A karon farko an bude wani baje kolin kayan tarin Musulunci da suke da dangantaka da birnin Qods mai alfarma da kuma masallacin aksa, da nufin raya ranar Qods ta duniya. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan baje kolin ya yi tasiri matuka wajen fadakar da dama daga cikin mutanen kasar dangane da tarihin birnin Qods da kuma dangantakarsa ta tarihi da musulmi. 466968