Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa; Shugaban kasar Rasha Dmitry Mevedev ya taya dukkanin al'ummar musulmi murnar salla, kamar yadda wata sanarwa ta nuna daga fadar shuban na Rasha. Bayanin ya ci gaba da cewa a cikin bayanin shugaban kasar ya bayyana idil fitr a matsayin wani buki na musamman mai matukar muhimmanci ga dukkanin musulmi, akan haka a matsaynsa na shugaban Rasha yana taya dukkanin musulmi murnar zagayowar wannan rana mai albarka. 467667