IQNA

An Sanar Da Sunayen Wadanda Za Su Halarci Gasar Kur'ani Ta Bahrain

13:01 - September 22, 2009
Lambar Labari: 1828723
Bangaren kasa da kasa; An sanar da sunayen wadanda za su halarci gasar karatun kur'ani da hardarsa a kasar Bahrain, wadda aka yi lakabi da gasar kyautata sauti, wanda aka fitar a jiya.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga jaridar alwasat ta kasar Bahrain cewa; An sanar da sunayen wadanda za su halarci gasar karatun kur'ani da hardarsa a kasar Bahrain, wadda aka yi lakabi da gasar kyautata sauti, wanda aka fitar a jiya. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasa za ta hada bangaren makaranta maa da mata, da shekarunsu suka kama daga goma sha shida zuwa 25, sai kuma bangarorin da za su gudanar da gasar zai shafi harda da karatu, da kumatajwidi, wato kyautata karatu. 467671

captcha