IQNA

Taron Kasa Da Kasa Kan Kokarin Malaman Kirwan A Addinin Musulunci

13:00 - September 22, 2009
Lambar Labari: 1828729
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani tarn kasa da kasa dangane da yadda malaman addinin Musulunci na birnin Kirwan da ke kasar Tunisia suka taka rawa wajen yada ilimin addinin Musulunci a duniya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na kungiyar raya ilmi da al'adun Musulunci ta duniya ISESCO cewa; Za a gudanar da wani tarn kasa da kasa dangane da yadda malaman addinin Musulunci na birnin Kirwan da ke kasar Tunisia suka taka rawa wajen yada ilimin addinin Musulunci a duniya. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan wannan taron da za a gudaa a karshen watannan nan Satumba, zai mayar da hankali ne kan rubuce-rubucen da malaman wannan birni suka yi da kuma tasiinsa wajen yada ilimin addinin Musulunci. Taron zai samu halartar malamai dam asana tarihi. 467502



captcha