IQNA

Makarncin Kur'ani Bairaniye Ya Zo Na Daya A Gasar Kur'ani Ta Alkauthar

17:17 - September 23, 2009
Lambar Labari: 1829320
Bangaren kasa da kasa; Makarancin kur'anin nan dan kasar Iran Jasim Musawi shi ne ya lashe gasar karatun kur'ani ta tashar talabijin din alkauthar da aka gudanar a matsayi na kasa da kasa a bangaren tajwidi.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na shurok online cewa; Makarancin kur'anin nan dan kasar Iran Jasim Musawi shi ne ya lashe gasar karatun kur'ani ta tashar talabijin din alkauthar da aka gudanar a matsayi na kasa da kasa a bangaren tajwidi. Bayanin ya ci gaba da cewa; wadanada suka gudanar da wannan gasar sun shiga cikin gasar net a hanyar wayar tarho, inda sukan yi karatu kai tsaye alkalan gasar suna suna yin alkalanci ana kallonsu a tashar talabijin, daga karshe dai an bayar da matsayi na farko ga jasim Mosawi, matsayi na biyu ga wata 'yar aljeria, matsayi na uku kuma ga 'yar kasar masar. 468048



captcha