IQNA

17:17 - September 23, 2009
Lambar Labari: 1829321

Dubban Musulmi Sun Gudanar Da Sallar Idi A kasar Birtaniya

Bangaren kasa da kasa; Dubban musulmi ne suka gudanar da sallar idi a birnin London na kasar Birtaniya bisa limancin fitaccen malamin nan Mu'azzi,

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na IC-EL cewa; Dubban musulmi ne suka gudanar da sallar idi a birnin London na kasar Birtaniya bisa limancin fitaccen malamin nan Mu'azzi, wakilin jagoran juyin juya halin musulunci a kasar Birtaniya. Bayanin ya ci gaba da cewa a lokacin da yake gabatar hudubar sallar idi ya bayyana cewa babban sirrin kara yaduwar addinin musulunci a cikin kasashen turai ba wani abu ban e illa adawar da ake nuna wa addinin musulunci ido rufe a cikin wadanan kasashe. 468052



captcha