Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran Nasij cewa; Za a gudanar da wani zaman taro tsakanin mabiya addinin musulunci da kuma mabiya addinin kiristanci a kasar Jamus a cikin watan Oktoba mai kamawa. Da nufin kawo karshen sabanin da ake samu tsakanin mabiya wadannan addinai. Bayanin ya ci gaba da cewa za a gudanar da wannan taro mai matukar muhimmanci ne a ranar 8 ga watan gobe, wanda zai samu halartar wakilan cibiyoyin musulunci a kasar da kuma wakilan majami'oi. 468139