IQNA

Shugabannin Addinai Za Su Gudanar Da Zamansu A Kasar Amurka

17:16 - September 23, 2009
Lambar Labari: 1829325
Bangaren kasa da kasa; Jagororin addinai za su gudanar da zamansu a birnin Pestburg na kasar Amurka, domin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci matsalolin da ke ci ma al'ummomin duniya tuwo a kwarya.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na jaridar Christian post cewa; Jagororin addinai za su gudanar da zamansu a birnin Pestburg na kasar Amurka, domin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci matsalolin da ke ci ma al'ummomin duniya tuwo a kwarya. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro zai samu halartar jagorin addinan musulunci, kiristsnci, yahudanci da ma wasu addinan, inda za su tattauna dangane da irin rawar da kowannansu ya kamata ya taka domin warware da dama daga cikin matsalolin da ke cima al'ummomin duniya tuwu a kwarya. 468190



captcha