Bangaren al'adu da fasaha; An bude reshen kamfanin dillancin labaran Iqna a kasar Tanzania, wanda kuma wannan shi ne reshe na goma da wannan kamfanin dillancin labarai yake da shi a kasashen ketare.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa; An bude reshen kamfanin dillancin labaran Iqna a kasar Tanzania, wanda kuma wannan shi ne reshe na goma da wannan kamfanin dillancin labarai yake da shi a kasashen ketare. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan reshe an bude ofishinsa ne a birnin Darsalam, babban birnin kasar Tanzania, wanda zai rika hada dukkanin labarai da suka danganci lamurran kur'ani da musulunci a kasar da ma wasu kasashen nahiyar nahiyar Afirka. Bugu da kari kuma wannan ofishi zai rika gudanar da wasu daga cikin harkokinsa na tsibirin Zenzibar na kasar Tanzania. 468088