IQNA

Kafa Bankin Musulmunci A Birnin Moscow Na Kasar Rasha

11:04 - September 24, 2009
Lambar Labari: 1829388
Bangaren kasa da kasa; Elexendar Toshian daya daga cikin manyan jami'ai a majalisar dattijan kasar rasha ya bayyana cewa, kafa bankin musulunci a kasar Rasha na tattare da gagarumin muhimmanci ta fuskar tattalin arzikin kasar rasha.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran Rasha cewa; Elexendar Toshian daya daga cikin manyan jami'ai a majalisar dattijan kasar rasha ya bayyana cewa, kafa bankin musulunci a kasar Rasha na tattare da gagarumin muhimmanci ta fuskar tattalin arzikin kasar rasha. Bayanin ya ci gaba da cewa kafa wannan banki zai taimaka ma 'yan kasuwa musulmi na kasar Raha wajen yin mu'amalar kudi hankali kwance, kamar yadda duk mai bukata ma zai iya yin mu'amala da wannan banki. 468641
captcha