Bangaren al'ada da fasaha: an gudanar da taron hadin guiwa tsakanin shugaban kungiyar hadin kan kasashe musulmi da shugabannin kasashen musulmi.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta watsa rahoton cewa; wannan taro an yi shi a a gefen taron shekara-shekara na ma'aikatar harkokin kasashen musulmi mambobi a cikin kungiyar da aka gudanar a kasar suriya. A lokacin wannan ganawa an tabo harkoki na bai daya da suka shafi kasashen musulmi da yadda za a binkasa su a nan gaba.
468186