Banagaren kasa da kasa" mu'assisar yada al'adu a birnin Dubai a wani shiri na karfafa guiwa ga wasu shirya fina-finai na musulmi ta bada kyautar dala miliyan daya ga fim din da ta fi nuna kyawawan dabi'u a watan azumin ramadana.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga jaridar hadaddiyar daular larabawa Albayan ta watsa rahoton cewa;Ahmad Abdallah Alsheikh mamba a wannan mu'assisar ya bada labarin cewa; mu'assisar yada al'adu a birnin Dubai a wani shiri na karfafa guiwa ga wasu shirya fina-finai na musulmi ta bada kyautar dala miliyan daya ga fim din da ta fi nuna kyawawan dabi'u a watan azumin ramadana ya kuma kara da cewa hakan zai kara jan hankalin sauran sanin muhimmancin kula da kyawawan halaye a kowane irin yanayi da mutum ya samu kansa a ciki.
468911