Bangaren kasa da kasa; An kawo karshen gasar karatun kur'ani mai tsarki da aka gudanar a kasar Qatar, wanda kuma wannan shi ne karo na gom ada ake gudanar da irin wannan gasa ta shekara-shekara a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa; a cikin wani rahoto da ya nakalto daga jaridar raya ta kasar Qatar an bayyana cewa; An kawo karshen gasar karatun kur'ani mai tsarki da aka gudanar a kasar Qatar, wanda kuma wannan shi ne karo na gom ada ake gudanar da irin wannan gasa ta shekara-shekara a kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasa ta samu halartar makaranta da kuma mahardata, wadanda aka girmama su bayan kammala gasar ta hanyar ba su kyaututtuka. 469270