Kamfanin dillancin labaran Iqna ya lakalto daga shafin internet na Nasij cewa; Jami'ar Azhar da ke birnin alkahira na kasar Masar ta yi na'am da kafa dokar hana wulakanta addinai a kasar Ireland ta kudu, tare da bayyana hakan da cewa mataki ne mai kyau da zai kara kawo zaman lafiya tsakanin da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan mataki da gwamnatin Ireland ta dauka yana da matukar muhimmanci sauran gwamnatocin kasashen turai su yi koyi da shi. 469314