IQNA

Za A Gurfanar Da Dan Kasar Holland Mai Gaba Da Musulunci A Kotu

14:28 - September 27, 2009
Lambar Labari: 1830544
Bangaren kasa da kasa; Dan majalsar dokokin nan na kasar Holland Geert Wilders ami tsananin gaba dad a addinin Musulunci, zai gurfana a gaban kuliya.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga gidan talabijin din kasar Turkiya TRT cewa; Dan majalsar dokokin nan na kasar Holland Geert Wilders ami tsananin gaba dad a addinin Musulunci, zai gurfana a gaban kuliya bisa zarginsa da neman tayar da kayar baya a kasar ta hanyar nuna kyamar wani jinsin mutane da addininsu. Bayanin ya ci gaba da cewa jami'ai masu kula da harkokin shari'a na kasar ne suka bukaci da a gurfanar da shi domin hukunta shi kan laifukan nuna wariya da yake yi, wanda hakan ya sabawa dukkanin dokin kasar. 469582



captcha