Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Saphirnews cewa; Za a bude wata makarantar koyar da karatun kur'ani mai tsarki a gabacin birnin Paris na kasar Faransa, domin koyar da yaran musulmi karatun kur'ani mai tsarki. Bayanin ya ci gaba da cewa babbar cibiyar musulmi ta birnin Paris ita ce ta shiga gaba wajen ganin an aiwatar da wannan shiri kamar yadda aka tsara shi. Makarantar dai za ta kunshi ajuuwan kuyar da yara, kama daga 'yan shekaru uku har zuwa sama.kamar yadda za a rika koyar da su ilmomin ibada da dai sauransu. 469644