IQNA

ISESCO Za Ta Halarci Taron Addinai Da Za A Gudanar A Amurka

14:28 - September 27, 2009
Lambar Labari: 1830548
Bangaren kasa da kasa; Kungiyar kula da harkokin ilimi da al'adu na kasashen musulmi ISESCO za ta halarci taron mabiya addinai na kasa da kasa, da za a fara gudanarwa a babban zauren majalisar dinkin duniya.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga bangaren yada labarai na kungiyar hadin kan kasashen musulmi cewa; Kungiyar kula da harkokin ilimi da al'adu na kasashen musulmi ISESCO za ta halarci taron mabiya addinai na kasa da kasa, da za a fara gudanarwa a babban zauren majalisar dinkin duniya. Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai mayar da hankali ne wajen kara kusanto da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban daga kasashe daban-daban. 469749
captcha