IQNA

An Girmama Makarntan Kur'ani Bayan Kammala Gasa A Yaman

14:31 - September 28, 2009
Lambar Labari: 1831040
Bangaren kasa da kasa; An gudanar da wani taro domin girmama wadanda suka shiga cikin gasar karatun kur'ani a kasar Yeman, wanda talabijin din And ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran Yaman News cewa An gudanar da wani taro domin girmama wadanda suka shiga cikin gasar karatun kur'ani a kasar Yeman, wanda talabijin din And ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan dai ba shi ne karon farko da aka gudanar da irin wannan gasa ba, kuma za a ci gaba da gudanar da ita domin kara karfafa matasa makaranta kur'ani. 470140






captcha