IQNA

Za A Fara Gudanar Da Gasar Kur'ani A Saudiyya

14:31 - September 28, 2009
Lambar Labari: 1831041
Bangaren kasa da kasa; Za a fara gudanar da gasar hardar kur'ani da kuma karatu gami da tafsirin kur'ani a kasar saudiyya, wanda za a gudanar a birnin makka mai alfarma daga mako mai zuwa.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Nasij cewa; Za a fara gudanar da gasar hardar kur'ani da kuma karatu gami da tafsirin kur'ani a kasar saudiyya, wanda za a gudanar a birnin makka mai alfarma daga mako mai zuwa. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shi ne karo na talatin da daya da za a gudanar da wannan gasar kur'ani ta kasa da kasa a Saudiyya. Masu karatu da mahardata kur'ani daga kasa 115 ne za su halarci gasar. 470192



captcha